Mark 1

1Wannan itace farkon bisharar Yesu Almasihu, Dan Allah. 2kamar yadda aka rubuta cikin littafin annabi Ishaya. Duba, ina aika manzona, a gabanka, wanda zai shirya maka hanya. 3Akwai murya mai kira a jeji, tana cewa ka shirya hanyar Ubangiji. ka daidaita ta.

4Yahaya ya zo, yana baptisma acikin jeji yana wa’azin tuba, domin gafarar zunubai. 5Dukan kasar Yahudiya da mutanen Urshalima suka zo wurin sa, a ka kuma yi masu baptisma a kogin urdun. suna furta zunubansu. 6Yahaya yana saye da tufa ta gashin rakumi, yana kuma da damara ta fata a kugunsa, abincinsa fara ce da zuma.

7Yana wa’azi, ya ce “akwai mai zuwa a bayana wanda ya ke da iko fiye da ni. wanda ko maballin takalminsa ban isa in kwance ba. 8Ni ina yi maku baptisma da ruwa, amma mai zuwa a bayana zai yi maku baptisma da Ruhu Mai Tsarki‘’.

9Sai ya kasance a kwanakin nan Yesu ya zo daga Nazarat ta Galili, sai Yahaya ya yi masa baptisma a kogin urdun. 10Sa’adda Yesu ya fito daga ruwan, sai sama ta bude, sai Ruhu ya sauko a bisansa da kamanin kurciya. 11Sai wata murya ta zo daga sama, tana cewa, “Kai kaunataccen Dana ne. zuciyata ta na murna da kai kwarai‘’.

12Sai Ruhu ya iza shi zuwa jeji. 13Yana a jeji kwana arba’in, Shaidan yana jarabtar sa. Yana cikin jeji da dabobi, sai malaiku su ka yi masa hidima.

14Bayan da aka kama Yahaya, Yesu ya shiga kasar Galili yana wa’azin bisharar Allah. 15Yana cewa, “Lokaci ya yi, gama mulkin Allah ya kusato. Ku tuba ku bada gaskiya ga bishara”.

16Sa’adda ya ke wucewa a gefen takun Galili, sai ya ga Saminu da Andarawus, dan’uwansa suna jefa taru a teku, domin su masunta ne. 17Yesu ya ce masu ku zo, ku biyo ni, ni kuwa sai in maisheku masuntan mutane”. 18Nan da nan suka bar tarun su, suka bi shi.

19Sa’adda Yesu ya yi tafiya kadan, sai ya ga Yakubu dan Zabadi da Yahaya dan’uwansa; suna gyaran tarunsu a jirgin ruwa. 20Sai ya kira su, su kuwa suka bar mahaifinsu Zabadi a jirgin ruwan da ma’aikatansu, sai su ka bi shi.

21Da su ka shigo cikin kafanahum, a ranar asabar, Yesu ya shiga majami’a ya koya masu. 22Su ka yi mamakin koyarwarsa, domin ya na koya masu da iko ba kamar marubuta ba.

23A nan cikin majami’a akwai wani mutum mai kazamin ruhu, sai ya yi ihu da karfi. 24Yana cewa Ina ruwan mu da kai, Yesu Banazarat? Ka zo ne domin ka halakar da mu? Na san wanene kai. Kai ne Mai Tsarki na Allah”. 25Sai Yesu ya tsauta wa kazamin ruhun ya ce, “Ka yi shiru ka fita daga cikinsa”. 26Bayan da kazamin ruhun ya buga shi kasa, sai kazamin ruhun ya yi ihu sa’annan ya fita daga jikinsa.

27Sai dukan mutanen su ka yi mamaki kwarai, suna tambayar junansu menene wannan? wace sabuwar koyarwa ce da iko haka? har yana umartar kazaman ruhohi suna kuwa yi masa biyayya!” 28Nan da nan labarinsa ya bazu ko’ina a dukkan kewayen kasar Galili.

29Bayan da suka bar majami’a, sai su ka shiga gidan Saminu da Andarawus, suna kuma tare da Yakubu da Yahaya. 30Surikar Saminu tana kwance ba lafiya tana fama da zazzabi. Sai suka gaya wa Yesu game da ita. 31Sai ya zo, ya kama hannunta, ya daga ta, sai zazzabin ya sake ta, ta fara yi masu hidima.

32Da yamman nan, bayan da rana ta fadi, sai su ka kawo masa dukan marasa lafiya da masu fama da aljanu. 33Dukan mutanen garin su ka taru a bakin kofa. 34ya warkar da masu ciwo da yawa da masu chututtuka iri-iri, ya kuma fitar da bakaken aljanu, amma bai yarda aljanun su yi magana ba domin sun san shi.

35Ya tashi da sassafe, tun da sauran dare, ya tafi wurin da ba kowa, a can ya yi add’ua. 36Saminu da wandanda suke tare da shi suka neme shi. 37Suka sa me shi, sai su ka ce masa, “kowa yana nemanka”.

38Ya ce, bari mu tafi wani wuri, zuwa wadansu garuruwan da ke kewaye, Saboda in yi wa’azi a can kuma. Wannan shi yasa na zo nan‘’. 39Ya tafi dukan kasar Galili, yana wa’azi a majimi’un su yana kuma fitar da aljanu.

40Wani kuturu ya zo wurinsa. Yana rokonsa, ya durkusa. Ya ce masa, “in ka yarda kana iya warkar da ni. 41Sai ya yi juyayi, Yesu ya mi ka hannun sa ya ta ba shi ya na ce masa “Na yarda. Ka sarkaka”. 42Nan da nan kuturtar ta barshi, ya kuma sa mu tsarkakewa.

43Yesu ya yi masa gargadi sosai, ya salame shi. 44Ya ce masa “ka tabbata fa kada ka gayawa kowa, amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, sai ka je ka yi hadaya domin tsarkakewa kamar yadda Musa ya umurta, domin shaida.

Amma da ya fita sai ya fara gaya wa kowa, ya baza maganar a ko’ina, har Yesu bai iya tafiya a sake a garin ba. Ya tafi ya tsaya a wuraren da ba kowa, mutane kuwa su ka zo wurinsa daga ko’ina.

45

Copyright information for HauULB